Daga Habu Dan Sarki

An yi kira ga ‘yan Nijeriya mazauna birnin Landan da kewaye da su ziyarci sabon shagon soya balangu da aka bude a gini mai lamba 15 Titin Peckham Park, SE 15 6TR, shagon ‘Alhaji Suya,’ domin karfafa gwiwar dan Nijeriyar da ya fara wannan harka ta fawa a birnin.

Bayanan da suke fitowa daga Ingila na nuni da cewa, wannan bahaushe da ba a ambaci sunan sa ba, dan boko ne da ya ke da shaidar karatu ta digiri na biyu daga Jami’ar Greenwich ta Landan.

Shagon Alhaji Suya shi ne na farko a wannan yanki na Kudu Maso Gabashin birnin, wanda akasari ‘yan Nijeriya da suka fito daga yankunan Yarabawa da Inyamurai, mutanen Kalaba da ‘yan Edo sune suka fi yin harkokin kasuwanci da cin amfanin sa a wannan yankin.

┬ęZuma Times Hausa

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here