Daga Adamu Umar Kumo

Hukumar yaki da yi wa tattalin arziki ta’annati ta Nijeriya, wato EFCC, za ta sake gurfanar da tsohon Gwamnan jihar Gombe Sanata Danjuma Goje a gaban kotu a ranar 10 ga watan Afrilun wannan shekara da muke ciki bisa zargin da take masa na sama da fadin kudin jihar a lokacin da yake Gwamna da kudin ya kai kumanin Naira Biliyan 5.

EFCC za ta sake gurfanar da Danjuma Gojen ne tare da wasu mutane 3 da suka had’a da Alhaji Aliyu El-Nafaty, S.M. Dokoro da kuma Alhaji Sabo Tumu. Za su gurfana ne a gaban babbar kotun tarayya dake garin Gombe.

Sake gurfanarwar ya biyo bayan wasu gyara-gyare ne da EFCC ta yi wa tuhume-tuhumen da ake yi musu.

Shi dai Sanata Danjuma Goje ana tuhumar sa ne da karban bashi daga bankin Access har na naira biliyan 5 bayan ya yi sojan gona ta hanyar sanya hannu na bogi akan takardun da suka taimaka masa ya karbi bashin kudaden don yin ayyukan raya kasa amma ya karkatar da su ta wata hanya daban.

Tuhumar da ake yi wa Sabo Tumu na da alaka ne da kwangilar samar da abinci a gidan gwamnatin jihar Gombe. Haka kuma EFCC na tuhumar S.M. Dokoro ne da taimakawa wajen rarraba wasu motoci har guda 50 kirar Toyota Hiace mallakar jihar Gombe ga wasu mutane akan kudi naira miliyan 22 alhalin kiyasin kudaden motocin ya kai kimanin naira miliyan 250. Shi kuma El-Nafaty a nasa bangaren EFCC na tuhumar sa ne da hada baki da Danjuma Goje wajen karkatar da naira biliyan 1 da miliyan 600 daga hukumar ilimin bai daya na jihar Gombe wato SUBEB.

©Zuma Times Hausa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here