– An rantsar da shugabannin majalisun kananan hukumomi da aka zaba ranar asabar a birnin Kano domin su fara aiki daga yau litinin. Hukumar Zaben Jihar Kano ta ce APC ce ta lashe dukkan kujerun shugabanni 44 da na kansiloli 484 a jihar.

– A Najeriya Sojojin Operation Lafiya Dole sun ceto wata tsohuwa da jikarta daga wani sansanin ‘yan Boko Haram da suka gano suka kona da maraicen jumma’a a cikin dajin Sambisa.

– A Najeriya Sojoji sun yi kwanton bauna a ‘yan Boko Haram a Goniri a Jihar Yobe, inda wata tankar soja ta take wata motar yakin Boko Haram dake dauke da bama-bamai.

– Kungiyar dattawan arewacin Najeriya, ta kafa wani sashi a kungiyar da aka dorawa nauyin samar da hanyoyin warware matsalolin da suka shafi siyasa da sauran al’amuran gudanarwa, da ke ci wa yankin arewacin kasar tuwo a kwarya.

– Tsohon gwamnan jihar Jigawa, Alhaji Sule Lamido ya ce, sai shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya koma babbar jam’iyyar adawa ta PDP kafin ya ba shi shawarar magance wasu matsalolin da ake fuskanta a gwamnatinsa.

– Gidauniyar Mo Ibrahim da ke karrama shugabannin kasashen Afrika da suka taka rawar gani kuma suka sauka a karagar mulki ba tare da haifar da matsala a kasashensu ba, ta bayyana tsohuwar shugabar Liberia, Ellen Johnson Sirleaf a matsayin wadda ta lashe kyautar mai dauke da Dala miliyan 5.

– Shugaban Jam’iyyar ANC mai mulki a Afirka ta Kudu Cyril Ramaphosa ya amince cewar kawunan ‘ya’yan jam’iyyar a rarrabe suke, yayin da jam’iyyar ke ci gaba da fafutukar kawar da shugaban kasar Jacob Zuma daga kujerarsa, in da za ta gudanar da wani zama a yau don fayyace makomarsa.

– Dubban ‘yan kasar Italiya sun gudanar da zanga-zangar nuna kyama ga akidar nuna wariyar launi a garin Macerata, inda a makon da ya gabata wani dan bindiga ya bude wuta kan bakin-haure ‘yan nahiyar Afrika.

– A jiya Lahadi wani jirgin Fasinjan Rasha  ya yi hatsari dauke da mutane 71. Jirgin ya yi hatsari ne dab da birnin Moscow na kasar ta Rasha. Jami’an agaji sun soma isa inda  jirgin saman fasinjan kasar Rasha ya yi hatsari.

– Masu gudanar da bincike a Rasha na karade wurin da jirgin saman fasinjan kasar ya yi hatsarin da ya sabbaba mutuwar daukacin mutane 71 da ke cikinsa a kusa da birnin Moscow.

– Mai horar da Manchester United, Jose Mourinho ya ce, ko da kungiyarsa za ta shafe tsawon sa’oi 10 tana fafatawa da Newcastle, ba za ta zura kwallo guda ba a St James Park. Mourinho ya bayyana haka ne bayan Manchester United ta sha kashi da ci daya mai ban haushi a karawar da ta yi da Newcastle a jiya a gasar firimiya ta Ingila.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here